Matsanancin Soyayyar Da Rakiya Moussa Ta Fada A Ciki Nafila Ce Akan Tawa, Domin Ni Har Saida Aka Kwantar Da Ni A Asibiti
Daga Sufiyanu Nura
Hmmm!😭😭
Ban so yin wannan maganar ba, saboda ni ba na zancen soyayya, saboda gudun yin rashin kunya a bainar jama'a tunda akwai iyaye na a sahar, shiyasa ban taɓa yi ko bada labari ba.
Idan ana wani zancen shiru kawai ake yi, na rantse da Allah shekara ɗaya da rabi da ta wuce ban zaci zan rayu ba, duk dalilin So, domin fadeelat ta samu wanda zata Aura wanda ba niba 😭💔
Idan da a ce zan bada labarin soyayya ta da Fadeela ( rayuwa ta) to' da, da yawan masu karatu sai sun zubar min da hawaye saboda ciwo, na so Fadeela son da ban yi wa kaina ba ma, ina jinta a rai na har gobe ba kuma zan daina ba, koda ace na daina sai dai idan ban tuno ta ko ta kirawoni ba! 💔
So bala'i ne! 😭😭
Wannan hoton na ƙasa shine lokacin da, aka kai ni asibiti domin samun kulawar gaggawa bayan mahaifin Fadila ya kira ni a waya zuwa gidansa ya sanar da ni cewa jiya ya karbi kudin auren Fadila daga hannun wani.
Muna matuƙar ƙaunar juna har gobe. 💔 Kuma ban daina kallon mahaifinta a matsayin uba ba har gobe. 💔