Bani da wata alaƙa ta soyayya

 DA DUMI-DUMI: Ba Ni Da Wata Alaka Ta Soyayya Da Rakiya Moussa Face Mutunci, Cewar Mawaki Hamisu Breaker


Bayan tsawon lokaci da aka dauka ana zargin cewa da shi jarumar take a yayin wata hira da abokiyar aikinta Hadiza Gabon ta yi da ita, saidai Mawakin ya fito ya wanke kansa kamar haka;

"Assalamu alaikum masoyana tare da fatan kun sha ruwa lafiya, dazu wasu daga cikin masoyana suka ja hankali akan wannan batun da yake ta yawo cewa Rukayya Yusuf ƴar asalin Niger wadda Hadiza Aliyu tanyi hira da ita, wasu mutane na  cewa wai da ni ta yi soyayya kuma har na juya mata baya. Sam-sam wanna maganar ba haka take ba, hasali ma ni babu wata alaƙar soyayya tsakanin mu sai dai mutunci".

Post a Comment

Previous Post Next Post